Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Bauchi (SEMA) ta kai ziyarar gani da ido yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a dukkanin kananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi.
Shugaban hukumar gudanarwa ta SEMA, Yusuf A. Danlami Alkaleri, ya bayyana haka cikin hirarsa da manema labarai a Bauchi, ya yaba da kokarin jami’an hukumar ta SEMA a duk tsawon lokaci da aka dauka ambaliyar ruwa na mamaye wasu sassan Jihar Bauchi da kuma wasu jihohin, amma basu zauna ba sun tashi tsaye sun yi ta kai ziyara ba dare ba rana tare da bayar da tallafin kayan agajin da aka samar daga gwamnati.
Yace, ziyarar ta kasance domin duba yadda ambaliyar ruwan ta shafa, kuma gwamnati ta yi amfani da abin da aka samar don taimakawa.
Ya kara da cewa, za a ci gaba da samar da wasu kayayyakin don rabawa, saboda haka mutane su kara hakuri.
Shugaban ya shawarci jama’a su rika bin umarnin masana hasashen yanayi don kare kai daga hadurran ambaliyar ruwa da gurbatar muhalli.
Alhaji Abdullahi Alkaleri yace an kaddamar da su ranar 16/4/2024 a karkashin ma’aikatar jinkai ta jiha wacce Hajiya Hajara Yakubu Wanka ke jagoranta.
Shugaban hukumar gudanarwa ta hukumar bayar da agajin gaggawa ya kara da cewa tun lokacin da gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya dora musu wannan nauyin sun himmatu wajen ganin sun sauke, musamman ganin sun zo aikin a lokacin da hukumar yanayi ta kasa NIMET a ranar 20/2/2024 ta yi hasashen za a iya fuskantar matsalar ambaliyar ruwa a jihohi 31 kuma ciki har da Bauchi.
A karon farko an samu kalubale a Kirfi. yadda aka samu tsawa da ruwa da iska a Dewu da Bara da sauran yankunan karkarar Kirfi da Alkaleri kuma mutane sun wahala.
Abdullahi Danlami ya ce matsalar ta ci gaba da hauhawa har zuwa karamar hukumar Darazo da Misau da Giyade da Gamawa da Katagum da Zaki da Shira da Jama’are da sauran wuraren da abin ya shafa.