
Daga Abubakar Rabilu, Gombe
Wata kungiyar siyasa mai suna Nigeria Forward ta yi kira ga ‘yan siyasar Arewa da su dakatar da neman shugabancin Najeriya a zaben 2027, tana mai cewa ya kamata yankin ya jira har zuwa shekarar 2031.
Mataimakin jagoran kungiyar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce hakan zai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar kammala wa’adinsa na shekaru takwas tare da ci gaba da aiwatar da manufofin da gwamnatinsa ta fara.

Waiya, wanda kuma shi ne Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, ya bayyana hakan ne yayin bikin kaddamar da kungiyar a hukumance.
Ya ce tun bayan komawar Najeriya tsarin dimokuradiyya a 1999, fahimtar sauya shugabanci tsakanin Arewa da Kudu ta taimaka wajen daidaita rabon mulki da karfafa hadin kan kasa.
“Bai kamata Arewa ta nemi karbar shugabancin kasa a 2027 ba bayan shekaru hudu kacal na gwamnatin yanzu. Ya kamata a bar Tinubu ya kammala shekaru takwas,” in ji shi.
Waiya ya bukaci ‘yan siyasar Arewa da su fifita hadin kan Najeriya da ci gabanta a kan muradun siyasar zabe.

Ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji matsalolin tattalin arziki da tsaro, yana mai cewa wasu daga cikin matakan da ta dauka sun fara kawo sauye-sauye.
Daga cikin matakan da ya ambata akwai karin kudaden da ke zuwa ga jihohi da kananan hukumomi, cin gashin kan kananan hukumomi da kuma shirin kafa ‘yan sandan jihohi.
Ya ce wadannan sauye-sauye na iya taimakawa wajen inganta shugabanci, tsaro da tattalin arzikin kasa idan aka aiwatar da su yadda ya kamata.
A nasa bangaren, Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Dakta Kingsley Tochukwu Udeh, ya ce gyare-gyaren gwamnatin tarayya na da nufin bunkasa ababen more rayuwa, samar da ayyukan yi da kara habaka tattalin arziki.
Udeh ya ce bai kamata a mayar da batun ci gaban Najeriya, musamman na Arewa, zuwa kalaman siyasa kawai ba, sai an duba ayyukan da ake gudanarwa da irin tasirin da suke yi ga al’umma.

Ya bayyana cewa inganta hanyoyi zai taimaka wajen hada manoma da kasuwanni, yayin da layin dogo zai rage kudin jigilar mutane da kayayyaki.
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayan sake zaben Tinubu a 2027 domin ci gaba da aiwatar da manufofi da gyare-gyaren da gwamnatin ta fara.


