Daga Wakilinmu
Matatar mai na Dangote ta fara tace man dizel da na jirgin sama.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya bayyana matukar godiyarsa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu saboda gagarumar gudunmuwa da goyon baya da kuma shawarwarin da ya bayar domin ganin wannan aikin ya tabbata.
Dangote ya kuma gode wa kamfanonn NNPC da NUPRC da NMDPRA da daukacin ‘yan Najeriya saboda goyon baya da kuma imanin da suka yi da wannan aiki mai dimbin tarihi.
“Muna kuma godiya ga shugaba Bola Tinubu saboda goyon bayan da ya bayar domin ganin wannan mafarkin ya zama gaskiya. Wannan fara aikin tace mai da matatar ta yi, ya faru ne saboda shugabancinsa nagari da hangen nesansa da kuma sauraron bayani da yake yi. Shawarwarin da ya rika bayarwa a kowane mataki sun taimaka wajen kawar da duk wata matsala tare da gudanar da aikin cikin hanzari.”
Muna kuma gode wa kamfanonin NNPC da NUPRC da NMDPRA saboda goyon bayan da suka ba mu. Wadannan kamfanoni sun ba mu cikakken goyon baya a yayin wannan tafiya mai tarihi. Muna kuma godiya ga daukacin ‘yan Najeriya saboda goyon baya da kuma imanin da suka yi da wannan aikin.”
“Mun fara aiki ne da tace man dizel da man jirgin sama, kuma ana sa ran a cikin wannan watan man zai shiga kasuwanni da zarar mun samu amincewar haka.”
“Wannan babbar rana ce ga Najeriya. Mun yi farin ciki da kaiwa wannan muhimmin matakin. Wannan babbar nasara ce ga kasarmu, domin an nuna cewa za mu iya tsarawa tare da aiwatar da manyan ayyuka.”
Zuwa yanzu matatar ta samu gangar danyen mai miliyan 6 a ma’ajiyarta guda biyu da ke kilomita 25 tsakaninsa da bakin ruwa. An samu kason danyen mai na farko ne a ranar 12 ga watan Disambar 2023, a yayin da aka samu kaso na 6 a ranar 8 ga watan Janairun 2024.
Matatar za ta iya loda wa tankoki dubu 2 da 900 mai a kullum. Kuma man da matatar za ta samar zai yi daidai da tsarin Euro V. Sannan tsarin matatar ya yi daidai da ka’idar Bankin duniya da US EPA da ka’idar fitar da hayaki na tarayyar turai da kuma sashin kula da gidajen mai (DPR), saboda an samar da ingantattun kayayyaki na zamani.”
Haka kuma dole ne in mika godiyarmu ga bankunanmu da wadanda suka bayar da kudinsu, saboda juriya da hakurin da suka nuna. Haka kuma muna godiya ga gwamnatin jihar Legas , a karkashin jagorancin Babajide Sanwo-Olu wanda ya jajirce wajen ganin an kawar da duk wata matsala da ta taso a yayin gudanar da wannan aikin. Muna godiya gare shi kwarai.”
Haka kuma ina godiya ga al’ummomin da ke kewaye da matatar da sarakunansu, saboda dauriya tare da hakurin da suka nuna, da kuma sha’awar da suka nuna na yin aiki da mu. Su ma ma’aikatanmu sun bayar da gagarumar gudunmuwa wajen samun nasarar wannan aikin. Ina matukar godiya a gare su.”